1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta baci a Turkiya

Abdourahamane HassaneJuly 21, 2016

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya ayyana dokar ta baci ta tsawon watannin uku bayan yunkurin juyin mulki da ya ci tura wanda wasu sojojin suka yi a makon jiya.

https://p.dw.com/p/1JSwr
Türkei Türkischen Präsident Tayyip Erdogan bei der Pressekonferenz
Hoto: Reuters/U. Bektas

Gwamnatin ta yanke wannan shawara ce a karshen wani taron koli na hukumomin tsaro da na majalisar ministoci a birnin Ankara. Dokar ta bacin za ta ba da damar kaddamar da dokar hana fita da takaita izinin yin taruka da kuma yin zirga-zirga a wasu wuraran da aka tantance, ba tare da shugaban ya bi ta hanyar majalisar dokoki ba.

Yanzu haka tun bayan yunkurin juyin mulkin mutane kusan dubu 55 aka kama daga malaman makaranta da 'yan sanda da alkalai da sojoji, ake tsare da su wadanda ake zargi da hannu a lamarin.