An kafa dokar soji a Guinea Conakry | Labarai | DW | 13.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokar soji a Guinea Conakry

Sugaba Lansana Conte na kasar Guinea mai fama da rigingimun cikin gida ya kafa dokar soji a wannan kasa dake yankin yammacin Afrika ,akokarinsa na kawo karshen boren yunkurin kifar da gwamnatinsa daga bangaren kungiyoyin kwadago na kasar.Mai shekaru 72 da haihuwa,shugaba Conte dake zama shi kansa tsohon General na soji ,wanda ya dare karagar mulki,bayan kifar da wadda take ci shekaru 23 da suka gabata,ya umurcin rundunar sojin kasar dasu tsoma baiki domin kare kasar daga fadawa yakin basasa,tare da sanar da dokar hana fita na tsawon saoi 20,cikin kwanaki 11 masu gabatowa.Shugaban kasar ta Guinea ,wanda bai cika fita a kafofin yada labaru ba,yayi jawabi ta gidan talabijin na kasar,ya bayyana cewa daukan wannan mataki ya zamanto wajibi bisa laakari da haklin da kasar ta tsinci kanta ciki na asarar rayukan mutane dari da dukiyoyi a wata guda daya gabata.