An kafa dokar ko ta kwana a arewacin Nijar | Labarai | DW | 25.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokar ko ta kwana a arewacin Nijar

Shugaban kasar Nijar Mamadou Tanja ya aiyana yar kwarya kwaryar dokar ko ta kwana a arewacin kasar,yana mai baiwa rundunonin tsaro na kasar karin iko a yakinsu da Azbinawa yan tawaye.Cikin wani jawabi da yayi shugaban na nijar yace dokar zata yi aiki na tsawon watanni uku.Kungiyar yan tawaye ta MNJ dai ta kashe sojoji 45 tun daga watan fabrairu.

Wannan doka ta tanja ta baiwa rundunonin kasar damar kama yan tawaye da tsare su haka kuma tana da ikon rage zirga zirgan fararen hula kann manyan hanyoyi na arewacin kasar inda ake da arzikin uranium.