An kafa dokar hana fita a yankuna da dama na Iraqi, gabannin yanke wa Saddam Hussein hukunci da kotu za ta yi yau a birnin Bagadaza. | Labarai | DW | 05.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokar hana fita a yankuna da dama na Iraqi, gabannin yanke wa Saddam Hussein hukunci da kotu za ta yi yau a birnin Bagadaza.

Sa’o’i kaɗan kafin buɗe shari’ar tsohon shugaban ƙasar Iraqi, Saddam Hussein, yau a birnin Bagadaza, inda ake sa ran kotun za ta yanke masa hukunci, gwamnatin Iraqin ta kafa dokar hana fita a yankuna da dama na ƙasar. Ta kuma soke duk hutun jami’an rundunar sojin ƙasar, saboda fargabar idan an yanke wa Saddam hukuncin kisa, za a yi tashe-tashen hankulla a ƙasar.

Lauyoyin Saddam ɗin dai sun ce a tattaunawar da suka yi da shi jiya asabar, ya bayyana musu cewa a shirye yake ya mutu da daraja kuma ba da wata fargaba ko tsoro ba. Ya kuma ce Amirka za ta sha kaye a Iraqin, kafin ta janye dakarunta daga ƙasar cikin kunya.

A ci gaba da tashe-tashen hankullan da ake addabar birnin Bagadazan dai, ma’aikatar harkokin cikin gidan Iraqin ta ce mutane 7 ne suka rasa rayukansu jiya daddare, sa’annan wasu 20 kuma suka ji rauni, a wani harin rokoki da aka kai a unguwar Adhamiyya.