1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da zabe a Iraqi

Hauwa Abubakar AjejeDecember 12, 2005

An bude runfunan zabe na musamman a asibitoci,gidajen fursuna da sansanonin soji a zaben yan majalisar dokoki na Iraq

https://p.dw.com/p/Bu3T
jamian zabe
jamian zabeHoto: dpa

Kwanaki uku kafin sauran jamar kasar su jefa kuriunsu a wannan zabe,yan Iraqi da suke kwance a asibitoci da fursunonin da jamian suke kaddamar da wannan zabe wanda Amurka take ganin zai kawo karshen sojin kutse na sa kai wadanda ita Amurkan take ganin suke haddasa hare hare a kasar ta Iraqi.

Ya zuwa yanzu dai gwamnati ta kafa tsauraran matakai da dokoki kamar yadda ta kafa a lokuta biyu a zaben baya cikin wannan shekarar,domin abinda ta kira kare hare hare da rage zubarda jini a lokacin zaben na ranar alhamis.

Daga ranar laraba zaa rufe dukkan filayen jirgin saman kasar da bakin iyakokinta har sai ranar jumaa ko asabar,tare da kara lokacin dokar hana yawon dare da haramta daukar makamai ko bindigogi,ga dukkan jamaa har wadanda suke da lasisin yin hakan,yayinda kuma aka bayarda hutun kwanaki 5 ga yan kasar domin wannan zabe mai tarihi.

A ranar 15 ga watan oktoba majalisa ta jefa kuriar gudanar da wannan zabe ba tare da balain hare hare da aka saba a kasar ba.

Zaben na wannan mako,zai bude wani sabon shafi a tarihin Iraqi,biyowa bayan tashe tashen hankula da rudani na gaggauta hambarar da gwamnatin Saddam Hussein,kafa gwamnatocin wucin gadi sau biyu da kuma sabon kundin tsarin mulkin kasar a watan oktoba daya gabata.

Yayinda kurar zaben zata lafa,jamaar kasar Iraqi zasu samu kansu da sabuwar majalisar dokoki mai waadin shekaru 4 wadda ake sa ran zata samar da sabuwar alkibla ga kasar da alummarta suke cikin mummunar hali na rikicin akida daya kunno kai bayan hambarar da gwamnatin Saddam.

Komawa ga tafarkin demokradiya,ta hanyar tsara zabuka da tabbatar da jamaa da dama sun fita,suna matsayin wani bangare na manufar Amurka a yankin gabas ta tsakiya,yayinda take tsara hanyoyin da zata bi na ficewa daga Iraqi,wadda ita kanta ta san tilas ta fice ko ba dade ko ba jima.

Sai dai samun nasarar wannan zabe da samarda zaman lafiya mai dorewa a kasar, ya dogara ne akan fitowar yan sunni da shugabanninsu da suka janye daga zaben majalisar dokoki ta wucin gadi a ranar 30 ga watan janairu,zabe na farko cikin yanci tun fiye da shekaru 50.

A wannan karon dai masu jefa kuria miliyan 15 da rabi ake sa ran zasu jefa kuriar zaben membobin majalisar dokoki 275,wadanda hakkin nada sabon shugaban kasa da mataimakansa guda 2 ya rataya a wuyansu.

Daga nan kuma majalisar tana kwanaki 15 ta zabi Firam minista wanda shi kuma zai zabi ministoci da zai mika sunayensu gaban majalisa domin amincewarta.