1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da sabuwar majalisar Afghanistan

December 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvFn

An kaddamar da majalisar dokokin Afghanistan inda tuni mataimakin shugaban kasar Amurka Dick Chaney,ya isa kasar a yau jumaa,domin halartar bikin kaddamarda sabuwar majalisar dokoki ta farko cikin fiye da shekaru 30 tare kuma da ziyartar dakarun Amurka da ke kasar ta Afghanistan,bayan wata ziyarar ba zata zuwa Iraqi

Chaney tare da shugaba Karzai da wasu manyan jamian suka hallara wajen bikin rantsar da yan majalisar dokoki da aka zaba a watan satumba da ya gabata.

Rantsar da sabuwar majalisar,ta kammala taswirar siyasa da kasar tare da kawayenta kamar su Amurka suka tsara ne makonni kadan bayan hambarar da gwamnatin yan Taliban shekaru 4 da suka shige.

Kasar Amurkan dai tana da dubban sojojinta a kasar,wadanda suke ci gaba da farautar yan kungiyar Taliban da magoya bayansu,ciki har da membobin kungiyar AlQaeda.

A ziyaratasa ta kwana daya, mataimakin shugaban na Amurka zai gana da shugaba Karzai,kafin ya wuce zuwa Oman,Saudiya da kuma Masar.

A wani labarin kuma,gwamnan lardin Kunar a kasar ta Afghanistan Asaddullah Wafa, ya fadawa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa,wasu yan sanda 3 sun rasa rayukansu saoi kadan kafin bude bikin kaddamarda sabuwar majalisar,wanda yace yan kungiyar Taliban ne suka kai a wani shingen da yan sandan suka kafa.