An kaddamar da sabon tsarin daukar yan ci rani aiki a turai
October 23, 2007Talla
Jamian kungiyar taraiyar turai sun kaddamar da wani shiri na bada bada katin shaidar dan kasa mai suna blue card kwatankwacin na Amurka da ake kira green card domin janyo hankalin kwararrun maaikata su cike gurabub aiki a kasasshe 27 na kungiyar.Shugaban hukumar turai Jose Emmanuel Barroso yace wannan visa zai saukakawa kwarru hanyoyin samun aiki a kasashen turai,haka kuma zaa iya sabunta shi bayan kowane shekara biyu a koina cikin kasashen kungiyar.
Idan dai kasashen kungiyar sun amince da wannan shiri,zaa kawarda hanyoyi iri dabam daban har 20 na samun iznin zama ko aiki a kasashen turai.