An kaddamar da saban kundin tsarin mulki a Jamhuriya Demokradiyar Congo
February 18, 2006Talla
Shugaban Jamhuriya demokaradiyar Congo, Joseph kabila, ya kaddamar da saban kundin tsarin mulkin kasa, wadda ke matsayin mataki mai tasiri ta fannin girka inganttatar demokradiya a wannan kasa.
A watan desember ne da ya wuce, al´ummar ,ta kada kuri´ar amincewa da wannan saban kundin tsari mulki, da kashi 84 bisa 100, na wanda su ka yi zaben.
Kudin ya tanadi shinfida mulki mai ruwa 2 , bisa jagorancin shugaban kasa da Praminista.
Wannan mataki da aka cimma, zai bada damar shirya zabbuka daban daban a kasar, kamin karshen watan juni mai zuwa, wanda a sakamakon su, a ke kyauttata zaton Jamhuriya demokradiyar Congo ta bi sahun kasashen masu tafarkin demokradiya bayan yake yaken bassasa , da kuma mulki rikwan kwarya, na tsawan shekaru 3.