1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da bincike kan kisan Bhutto

December 28, 2007
https://p.dw.com/p/Chcg

Gwamnatin Pakistan ta kaddamar da bincike dangane da kisan gilla da akyiwa tsohuwar primiyan kasar Benezir Bhutto,ayayinda yansanda suka sanar dacewar suna da shaidar dake nuni dacewa shugaban kungiyar Alqaeda Baitullah Mehsud ,shine keda alhakin wannan kisa na jiya.Kakakin maaikatar harkokin cikin gida na pakistan Javed Iqbal Cheema,yace sun samu cikakkun bayani dake bayyana hakan da cewar“muna da ingantattun shaida dake nuni dacewar al-qaeda na kokarin tada zaune tsaye a pakistan,saboda zagewa da kasar tayi wajen yaki da ayyukan tarzoma“