An kaddamar da bincike game da take hakkokin bil adama a iraq | Labarai | DW | 15.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kaddamar da bincike game da take hakkokin bil adama a iraq

Faraministan kasar Iraqi Ibrahim Al Jafari ya bayar da umarnin gudanar da bincike game da zargin take hakkokin wasu fursunoni 173 da aka ce anyi a kasar.

Ibrahim al´jafari yace ya dauki wannan matakin ne bisa la´akari da cewa fursunonin nada alamar rashin koshin lafiya bisa azaba da suka sha a hannun wadanda suka tsare sun.

A cewar bayanai da suka iso mana dakarun sojin Amurka ne suka gano fursunonin a tsare a cikin wani daki dake ma´aikatar al´amurran cikin gida a birnin Bagadaza lokacin suna gudanar da sintiri.

Kafafen yada labaru sun rawaito cewa wasu jami´ai a cikin ma´´aikatar harkokin cikin gidan ne suka tsare wadan nan mutane tare da gana musu azaba.

A waje daya kuma hukumar kare hakkin bil adama ta Amnesty International yabawa Faraminista Jafari tayi bisa daukar wannan hukunci da cewa ya dace, to sai dai hukumar ta Amnesty ta bukaci da wannan kwamiti ya fadada aikin sa na gudanar da bincike akan duk wani zargi da akayi na take hakkokin bil adama a kasar.

An dai bawa kwamitin da aka doarawa alhakin gudanar da binciken makonni biyu don kammala binciken da kuma kawo rahoto.