1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kada kuri´ar amincewa da fadada magudanar ruwan Panama

October 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bueu
Tare da gagarumin rinjaye ´yan kasar Panama sun kada kuri´ar amincewa da shirin fadada magudanar ruwan kasar a wata kuri´ar raba gardama da aka kada a jiya. Kimanin kashi 79 cikin 100 na ´yan kasar ta Panama suka nuna amincewa da shirye shiryen fadada magudanar ruwan da aka fi sani da Panama Canal. Masu goyon bayan shirin sun ce fadada magudanar ruwan na da muhimmanci ganin karuwar manyan jiragen ruwa da ke amfani da wannan hanya kuma hakan zai samarwa kasar karin kudaden shiga.