1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jinkirta taron nukiliya na Iran

February 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9Y

Hukumar kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa,ta jinkirta yanke shawara akan ko ta mika Iran gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya akan batun nukiliya nata,zuwa gobe asabar idan Allah ya kai mu.

Kakakin hukumar kodayake bai baiyana dalilin samun wannan jinkirin ba.

A jiya dai hukumar ta fara muhawara akan mika Iran din gaban komitin sulhu saboda tsoron tana kera makaman kare dangi.

Ita dai Iran tayi gargadi a yau cewa,muddin dai aka mika ta gaban komitin sulhu,to kuwa ba zata sake duba batun amincewa kasar Rasha ta sarrafa sinadaren uraniyum na Iran din ba kamar yadda kasar Rashan tayi tayinsa tun farko.