An ji karar harbe harbe a kusa da fadar gwamnatin Amirka | Labarai | DW | 26.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ji karar harbe harbe a kusa da fadar gwamnatin Amirka

A wani mataki na riga-kafi ´yan sanda dake binciken rahotannin harbe harbe a wani gida dake kunshe da ofisoshin gwamnati a birnin Washington sun rufe ginin fadar gwamnatin Amirka. Kawo yanzu ba rahotanni na ko wasu sun jikata ko kuma aka kame dangane da harbe harben wanda ya auku da misalin 2 da rabi agogon GMT a wani wurin ajiye motoci dake cikin ginin Rayburn House Office. Kakakin ´yan sanda a fadar ta Capitol Kimberly Schneider ta nunar da cewa an dauki matakin ne bayan wani da bai bayyana sunansa ya buga musu waya yana mai cewa ya ji karar harbe harben bindiga a cikin ginin. ´Yan majalisar dattawa na wani zama lokacin hakan ya faru.