1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An je kotu tsakanin Kampanin Pfizer da gwamnatin Nigeria.

Kampanin Amurika mai sarrapa magunguna na zamani a Nigeria , wato Pfizer, yayi watsi da zargin da aka yi masa, na gwajin magunguna na jabu, a shekara ta 1996, a jihar Kano, wanda su ka yi sanadiyar mutuwar a ƙalla yara ƙanana 11, da kuma jikata da dama, daga jimilar yara 200 da aka yi gwajin kann su.

Bayan gwamnatin jihar Kano, itama gwamnatin Taraya, ta shigar da kara, inda ta buƙaci kampanin ya biya diyar dalla kussan milion dubu 3.

Gwamnati ta zargi Pfizer da leffika daban-daban har guda 29.

Kamapanin Pfizer ya ce, ya bada magungunan ga wannan yara, tare da amincewar iyayen su.

A halin yanzu dai, batu ya rage ga kotu,wace ke da yaunin yanke hukuci ƙarshe.