An hau tebrin shawarwari tsakanin Isra´ila da Palestinu | Labarai | DW | 09.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hau tebrin shawarwari tsakanin Isra´ila da Palestinu

Tawagogin Isra´ila da na Palestinu, na ci gaba da zaman taro a birnin Qudus, da zumar cimma daidaito a kan wani daftari na haɗin gwiwa wanda za su gabatar gaban taron ƙasa da ƙasa da Amurika ke shirin shiryawa, a wata mai zuwa,a game da rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Shugaban hukumar Palestinawa, da Praministan Isra´ila Ehud Olmert, da su ka gana da juna har sau 4, a tsukin wattani 2 da su ka wuce, sun bayyana aniyar gudanar da aiki kafaɗa da kafaɗa don cimma wannan buri.

To saidai masharanhanta a wannan yanki, sun bayyana shakku a game da kai wa ga wannan nasara, ta la´akari da mummunan saɓanin da ke akwai tsakanin su.

Kamar yadda a ka saba a tantanawa irin wannan, batutuwan da su ka dabaibaye ganawar sunhada da matsayin birnin Qudus, da yankunan Palestinu da Isra´ila ta mamaye, da kuma batun yan gudun hijira.