An harbi fitaccen dan adawa a Tanzaniya | Labarai | DW | 07.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An harbi fitaccen dan adawa a Tanzaniya

Wasu mutane da ba a kai ga tantance ko suwa ne ba ya zuwa yanzu sun kai hari da bindiga a gidan mataimakin madugun 'yan adawar kasar Tundu Lissu inda suka jikkata shi. 

Rahotanni daga kasar Tanzaniya na cewa wasu mutane da ba a kai ga tantance ko su wane ne ba  sun kai hari da bindiga a gidan mataimakin madugun 'yan adawar kasar Tundu Lissu inda suka jikatashi. 

A cikin wata sanarwa da jam'iyyarsa ta Chadema ta fitar a wannan Alhamis ta ce an harbi mataimakin shugaban nata a ciki da kuma a kafa kuma yanzu haka an garzaya da shi zuwa assibiti rai kwakwai mutu kwakwai. 

Tundu Lissu wanda dan majalisar dokoki ne a kasar ta Tanzaniya dan siyasa ne da ya yi fice wajen sukar lamirin Shugaban kasar tasu John Magufuli. Kuma an kai masa harin ne a da misalin karfe biyu agogon GMT a gidansa da ke a birnin Dodoma babban birnin kasar jim kadan bayan dawowarsa daga zaman majalisa.

Hukumar 'yan sandar birnin na Dodoma ta sanar da soma gudanar da bincike kan wannan batu.