1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harbe mataimakin Firaministan Iraki Abdel Mahdi har lahira

October 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvNG

A Iraqi an sake kai hari akan manyan jami´an gwamnati. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar wasu ´yan bindiga sun harbe dan´uwan mataimakin FM Iraqi Adel Abdel Mahdi a birnin Bagadaza. Shi dai Abdel Mahdi shi ne mai bawa FM Ibrahim al-Jafari shawara. A wani harin kuma mukaddashin ministan cinikaiyar kasar Kais Dawud Hasan ya samu rauni a wani kwantan bauna da ´yan tawaye suka kaiwa ayarin motocinsa. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce wasu ´yan bindiga suka bude wuta kan ayarin motocin ministan inda suka kashe biyu daga cikin masu tsaron lafiyarsa.