1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harbe masunta 5 a Najeriya

Ramatu Garba Baba
March 18, 2018

Ana zargin mayakan Boko Haram da halaka wasu masunta biyar da ake ganin na kokarin taimakawa gwamnatin kasar don gano inda aka nufa da 'yan matan sakandaren Dapchi da aka sace a watan da ya gabata a jahar Yobe.

https://p.dw.com/p/2uXNE
Tschad - Leben am Tschadsee
Hoto: picture-alliance/ dpa

An kai harin ne a jiya Asabar a yankin arewa Maso Gabashin kasar kamar yadda Alhaji Abubakar Gamandi shugaban kungiyar masu sayar da kifi na jahar Borno ya tabbatar, ya ce an bindige masunta har lahira a wani tsibiri da ake kira Tudun Umbrella da ke kusa da tafkin Chadi mai iyaka da Najeriya da Chadin da kuma kasar Kamaru.

Wannan ba shi bane karon farko da mayakan ke kai hari dama kashe masunta tun bayan da suka kaddamar da ayyukansu a yankin da ya janyo asarar rayukan mutane fiye da dubu ashirin a dalilin hare-haren kungiyar. Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya kai ziyara yankin ya dauki alkawarin ganin an kubutar da 'yan matan fiye da dari daya da mayakan suka yi awon gaba da su daga makarantan kwana da ke a garin Dapchi a jahar Yobe.