An harba makamai masu linzami daga Libanon zuwa Isra´ila | Labarai | DW | 17.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An harba makamai masu linzami daga Libanon zuwa Isra´ila

Wasu rokoki biyu da aka harba daga Libanon zuwa arewacin Isra´ila sun haddasa barna mai yawa amma ba su jiwa kowa rauni ba. Wannan dai shine karon farko da aka harba roka daga Libanon zuwa cikin Isra´ila tun bayan yakin da aka gwabza a bara tsakanin Isra´ila da sojojin kungiyar Hisbollah. Kafofin yada labarun Isra´ila sunce roka daya ta fadi kann wata masana´anta yayin da dayar kuma ta afkawa wata mota. An zargi wata kungiyar Falasdinawa ´yan aware a Libanon da hannu a wannan hari. Dukkan makaman dai sun fadi akan garin Kiryat Shemona. Kungiyar Hisbollah ta musanta hannunta a wannan hari. Tuni kuwa har Isra´ila ta kai dau fansa inda ta kai hari kan wasu yankunan dake cikin tsaunukan kudancin Libanon.