An hana kungiyoyin kwadagon Najeriya shiga yajin aiki | Labarai | DW | 17.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hana kungiyoyin kwadagon Najeriya shiga yajin aiki

Wata kotu a Najeriya ta hana kungiyoyin kwadago shiga wani yajin aikin gama gari don adawa da karin farashin man fetir.

Kotun ma'aikata ta kasa a Najeriya ta hana kungiyoyin kwadagon kasar kaddamar da wani yajin aikin gama gari don tilasta wa gwamnati ta soke karin kashi 67 cikin 100 da ta yi wa farashin man fetir. Kotun ta yanke wannan hukunci a kan kungiyoyin ma'aikata na NLC da TUC bayan karar da ministan shari'a Abubakar Malami ya shigar don neman a dakatar da kungiyoyin shiga yajin aikin. Da farko dai kungiyoyin sun umarci ma'aikata da su shiga yajin aiki daga ranar Laraba har sai gwamnati ta lashe amanta dangane da karin farashin mai da ta yi daga Naira 86.5 zuwa Naira 145 kowace lita. Mai shari'a Babatunde Adejumo ya ce kotun ta umarci kungiyoyin da su dakatar da yajin aikin. Tun a ranar Litinin ake wata ganawa tsakanin ma'aikatar kwadago da kungiyoyin ma'aikata da nufin hana shiga yajin aikin da gwamnati ta ce ka iya janyo wa kasar asarar miliyoyi dubbai na Naira.