1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hana Benazir ganawa da alakalan Pakistan

November 10, 2007
https://p.dw.com/p/CA3k

`Yan sanda a ƙasar Pakistan sun hana tsohuwar Firaministar ƙasar Benazir Bhutto ganawa da wasu alkalai da a ka kora daga kotun ƙoli ta ƙasar cikinsu kuwa har da babban alkalin alkalai Iftikar Chaudry.Kwana guda bayan dage daurin talala da a ka mata Benazir ta yi jawabi ga wani gun-gun yan jarida da suke zanga zangar tsauraran dokoki da a ka kafawa kafofin yaɗa labarai a kasar.

Musharraf ya sanarda dokar ta ɓacin ne musaman a cewarsa saboda harkokin tarzoma na ƙungiyoyin islama da ke kara ci gaba a ƙasar.Sai dai kuma jama’a da dama sun yi imanin cewa babban abinda ya sa ya ɗauki wannan mataki shine don kare kotuna daga yanke hukunci kan sake zaɓensa da a ka yi.