An hallaka wanda ya kai hari Jamus
December 23, 2016Mahukuntan Italiya sun tabbatar da hallaka mutumin da ake nema bisa zargi da hannu wajen hari a kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Anis Amri dan asalin kasar Tunisiya ya rasa ransa lokacin da ya yi musanyen wuta da 'yan sanda a birnin Milan na Italiya, wadanda suka tsare shi, sannan suka tambaye shi ya nuna katin shaida, amma maim akon haka sai ya bude wuta.
Dan sanda daya ya samu raunika, yayin da daya dan sandan ya samu nasarar kashe matashin da ake nema ruwa a-jallo. Ministan kula da harkokin cikin gida na ItaliyaMarco Minniti ya shaida wa taron manema labarai cewa tuni masu bincike suka tabbatar mutumin da aka harbe Anis Amri ne da ake nema sakamakon harin da aka kai kasar Jamus.
A cewar babban jami'in 'yan sanda na birnin Milan marigayin ya isa kasar ta Italiya ta jirgin kasa daga Faransa.