An hallaka Turawa biyar a kasar Habasha
January 18, 2012A kasar Habasha an hallaka mutane biyar yan yawon bude ido, wadanda yan asalin kashen Turai ne. Inda ake saran yan tawayen Habasha ne suka kai musu hari. Kakakin gwamnatin Habasha Bereket Simon ya fadawa manema labarai cewa, Turawan da aka hallaka sun hada da Jamusawa biyu, 'yan kasar Hungary kana da daya dan kasar Ostiriya, an kuma raunata Wani dan italiya da dan kasar Hungary. An kuma raunata wani dan kasar Italiya da daya dan kasar Hungary. Kawo yanzu ana ci gaba da yin garkuwa da Mutane hudu baki da dareban Turawan da kuma wani mai tsaron lafiyarsu. Farmakin dai an kai shine a lardin Afar dake kusa da kan iyakar Habasha da Eriteriya. Kasar Habasha ta dorawa makobciyar ta Eriteriya laifi, inda tace maharan suna samun mafaka ne a makobciyar ta, abinda kuma Eriteriya tace karya ce tsakwaron, wannan harkace da ta shafi cikin gidan kasar Habasha kawai.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu