1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka shugaban Taliban

Ahmed SalisuMay 22, 2016

Wani kusa a Kungiyar nan ta Taliban ya tabbatar da rasuwar jagoran kungiyar Mullah Akhtar Mansour a wani harin da sojin Amirka suka kai da jirgi maras matuki.

https://p.dw.com/p/1IsXS
Mullah Akhtar Mohammad Mansour
Hoto: Reuters

A daren jiya Asabar ce jami'an Amirka suka sanar da hukumomi Afghanistan cewar suna kyautata zaton cewar sun hallaka Mullah Akhtar din a wasu hare-hare da suka kai.Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta ce jiragenta sun kai hari kudancin Pakistan a wani yanki da ke kusa da kan iyakar Pakistan din da Afghanistan kuma nan ne suke tunanin sun hallaka jagoran na Taliban din.

Pentagon din dai ta ce an kai farmakin ne tare da izinin shugaban Amirka Barack Obama. Gwamnatin Afghanistan din ta tabbatar da rasuwar Mullah Mansour.