An halaka sojojin Taliban 40 a Afghanistan | Labarai | DW | 02.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An halaka sojojin Taliban 40 a Afghanistan

Dakarun Afghanistan da na ƙasashen ƙetare sun gwabza wani ƙazamin faɗa da mayaƙan Taliban a kudancin Afghanistan. Faɗan ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 40 inji jami´an Afghanistan. Dakarun haɗin guiwar sun shafe kwanaki 3 suna bata-kashi da sojojin ´yan tawayen a wani yanki mai tsaunuka dake cikin lardin Kandahar. Rahotannin sun ce an kuma kame ´yan tawaye 10. A kuma halin da ake ciki a Pakistan makwabciyar Afghanistan, fararen hula shida sun rasu lokacin da dakarun tsaro suka harba wasu rokoki da suka faɗi kan wata unguwa. Jami´ai sun ce rokokin sun afkawa wasu gidaje biyu da ke wani kauye a lardin arewacin Wazirista mai fama da tashe tashen hankula. Wannan lardi dai na matsayin wani sansanin ´yan Al-Qaida da sojojin sa kai na Taliban wadanda suka tsere daga Afghanistan.