An halaka masu zanga-zanga su kimanin 17 a kasar Guinea | Labarai | DW | 22.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An halaka masu zanga-zanga su kimanin 17 a kasar Guinea

A wani mataki na murkushe wani boren nuna kyamar shugaban jamhuriyar Guinea Lansane Conte ´yan sanda a kasar da ke yammacin Afirka sun kashe masu zanga-zanga su 17. wata sanarwa da likitoci da kuma kungiyoyin ma´aikata suka bayar ta ce ´yan sanda sun harbe masu zanga zangar ne har lahira a wajen Conakry babban birnin kasar. Tun fara wani yajin aikin gama gari da kungiyoyin ma´aikata suka kira kusan makonni biyu da suka wuce, an halaka mutane kimanin 30 a kasar ta Guinea. Jam´iyun adawa 14 na goyon bayan yajin aiki na sai baba ta gani, wanda aka shirya da nufin tilastawa shugaba Conte wanda ya haye kan karagar mulki tun a shekarar 1984, da yayi murabus. Ana zargin shugaban mai shekaru 72 da laifin cin hanci da rashawa da kuma rashin iya mulki.