An gwabza kazamin fada tsakanin ´yan Taliban da sojojin gwamnati | Labarai | DW | 15.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gwabza kazamin fada tsakanin ´yan Taliban da sojojin gwamnati

´Yan tawayen Taliban 41 da kuma ´yan sanda 6 aka kashe a wani mummunan fada da aka gwabza a kudancin Afghanistan a wani yanki inda shugaban taliban ya taba zama. An kwashe tsawon ranar jiya ana gwabza fadan a kudu maso yammacin birnin Kandahar. Jiragen yakin soji Amirka sun yi ta harba makamai masu linzami don marawa dakarun Afghanistan dake yaki da ´yan tawaye a kasa. Gwamnan birnin Kandahar Assadullah Khalid ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an halaka ´yan Taliban 41 sannan an jiwa da dama rauni. Sannan ´yan sanda shi da sun bakwanci lahira yayin da 9 suka samu raunuka. A halin da ake ciki an kame ´yan Taliban 13.