An gwabza fada tsakanin ´yan Fatah da ´yan Hamas | Labarai | DW | 28.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gwabza fada tsakanin ´yan Fatah da ´yan Hamas

A wata zanga-zanga da suka yi a birnin Gaza dubun dubatan magoya bayan kungiyar Fatah a cikin fushi sun yi kira ga shugabannin kungiyar da su yi murabus. Masu zanga-zangar sun zargi shugaba Mahmud Abbas da cin hanci da rashawa. Masu zanga-zangar sun yi jerin gwano zuwa gaban majalisar dokoki inda suka cunawa motoci wuta. Rahotanni daga kudancin Zirin Gaza sun ce a kalla mutane 9 sun samu raunuka a wani fada da aka gwabza tsakanin ´yan Fatah din da magoya bayan kungiyar Hamas, wadda ta lashe zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa da aka gudanar a ranar laraba.