An gurfanar da shugaban adawa na Uganda a gaban kotun soji | Labarai | DW | 24.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gurfanar da shugaban adawa na Uganda a gaban kotun soji

Rundunar sojin kasar Uganda ta zargi shugaban adawa na kasar da gudanar da aiyuka na ta´addanci a hannu daya kuma da mallakar makamai ba bisa ka´ida ba.

A wani dan kwarya kwaryar zama da kotun sojin ta gudanar, Mr Kizza Besigye yaki amincewa da zargin dan ta´addan da ake cajin sa dashi.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya rawaito lauyan Kizza, wato Sam Njuba na fadin cewa Mr Kizza yaki amsa laifuffukan da ake tuhumar sa da aikatawa ne, bisa dalilin cewa laifuffuka ne da kawai aka kago su aka kuma yaba masa.

Mr Kizza, wanda ya dawo kasar daga gudun hijira, a yanzu haka ya kasance a sahun gaba wajen adawa da mulkin shugaba Yoweri Museveni na tsawon shekaru 19.

Kafin dai wannan sabon caji da ake masa, Mr Kizza a yanzu haka kuma na fuskantar zargi na cin amanar kasa da kuma yiwa wata mata fyade a shekara ta 1997 a gaban kuliya.