An gudanar da zanga zanga a yankin Darfur na Sudan | Labarai | DW | 20.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gudanar da zanga zanga a yankin Darfur na Sudan

Wasu mutane da suka gudanar da zanga zanga a Al-geneina dake yankin Darfur na kasar Sudan sun halaka wani jami´in yan sanda guda ta hanyar jifa da duwatsu.

Al´amarin dai ya afku ne a lokacin da mutanen ke zanga zangar nuna adawa game da hare haren da yan gani kashenin kungiyoyin yan tawaye suka kawo musu, wanda hakan ya halaka mutane 20 ciki har da dattijai da kuma kana nan yara.

Wani jami´in bayar da agajin gaggawa a yankin mai suna Al Tijani Tajudden, ya shaidar da cewa masu zanga zangar sun aikata wannan danyan aikin ne don nuna fushin su game da asarar rayukan da sukayi na iyayen su da yan uwan su.