An gudanar da bukukuwan Sallah lafiya
July 7, 2016Talla
Al'ummar Musulmi a kasashen Najeriya, Nijar da kuma Ghana ta gudanar da bukukuwan Sallah karama cikin kwanciyar hankali da lumana duk da fargabar da aka yi ta yiwuwar fuskantar hare-haren ta'addanci musamman a Najeriya inda a shekarun baya 'yan Boko Haram suka yi nasarar kai hare-hare a wuraren idi a wasu jihohin Arewa maso Gabashin kasar.