1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gudanar da adu'oin zagayowar shekara guda da girgizar kasa ta Pakistan

October 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bugy

A yau jamaar kasar Pakistan suke gudanar da adduoin zagayowar shekara guda da girgizar kasa da tayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 73,000.

Jamaa da dama sun hallara a masallatai koina cikin kasar domin yin adduoi ga wadanda suka rasa rayukan nasu da kuma wadanda suka tsira da ransu da yawancinsu har yanzu basu da matsuguni.

A jiya asabar ne wadanda suka tsira daga girgizar kasar suka gudanar da zanga zanga bakin majalisar dokokin kasar a birnin Islamabad,suna masu zargin jamian dake kula da sake gina masu matsuguni da laifin cin hanci.

Maaikatan agajai da sunce kimanin mutane miliyan 1 da dubu 800 suke fuskantar matsanancin sanyi da cututtuka cikin lokacin sanyi na bana.

Sai dai shugaba Parvez Musharraf yace mutane 35,00 kadai zasu kasance cikin tantuna a yankuna dake da sanyi a kasar.