1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An girka komitin sulhunta rikicin siyasa a ƙasar Togo

April 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0u

Jam´iyun siyasa a ƙasar Togo sun zaɓi shugaban jam´iyar CAR mai adawa, a matsayi shugaban komitin sulhu da sasanta rikicin siyasar ƙasa.

Ranar juma´a da ta gabata ne, yan siyasr da ƙungiyoyi masu zaman kansu , su ka koma tebrin shawarwari, da zumar warware ringinginmun siyasa, da su ka biwo bayan zaɓen shugaban ƙasa, da kashe- kahen jama´a, bayan mutuwar mirganyi Yasimbe Eyadema, ranar 5 ga watan Februaru, na shekara ta 2005.

Ɓangarorin na burin cimma matsa ɗaya, a game da batutun da su ka shafi kwaskwarima ga kunɗin zaɓe na ƙasa da shirye shiryen zaɓen yan majalisun dokoki da za a gudanar.

Hukumomin bada lamani na dunia da ƙungiyar gamaya turai,sun gitta shariɗin kyauttata harakokin siyasa, a ƙasar, kamin su bada taimakon kuɗaɗen tafiyar da ayyuka.