An gargadi Trump kan cirewa Rasha takunkumi | Labarai | DW | 27.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gargadi Trump kan cirewa Rasha takunkumi

Fitaccen dan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican a Amirka wato Sanata Johm McCain ya gargadi Shugaba Donald Trump da ya guji janye takunkumin da Amirka ta kakabawa Rasha.

Sanata McCain wanda ke da karfin fada a ji a fagen siyasar Amirka na wadannan kalamai daidai lokacin da ake rade-radin cewar gwamnatin Trump za ta kawar da takunkumin da ke kan Rasha din, lamarin da ya sanya ya ce muddin aka dau wannan matakin to majalisar dattawan kasar za ta maidawa shugaban martani kakkausa.

A wani jawabi da ya yi ga manema labarai, McCain ya ce muddin Trump ya janyewa Moscow takunkumin da aka sanya mata to shi da takwarorinsu na majalisar dattawa za su yi aiki tare wajen ganin sun dau matakin da zai kai ga maida takunkumin da ke kan din Rasha din ya zama doka.