An gargaɗi Iran da ta daina katsalanda a Iraƙi | Labarai | DW | 11.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gargaɗi Iran da ta daina katsalanda a Iraƙi

Sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice ta gargadi Iran cewa Amirka ba zata zura ido tana ganin gwamnati a Teheran na marawa masu kaiwa Amirka hari a makwabciyar Iran wato Iraqi ba. Rice ta kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da shirin ta na nukiliya. A gun wani taron manema labarai a Washington Rice ta kuma ba da sanarwar nadin wani dan diplomasiya da yayi ritaya wato Timothy Carney don ya jagoranci wani sabon shirin Amirka na tallafawa tattalin arziki da shirin wanzar da zaman lafiya a Iraqi.