1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano wasu sassan jirgin Malesiya da ya bace

Cibiyar kula da harakokin tsaro a fannin sufuri ta Ostareliya ta ATSB ta bayyana hakana cewa an gano sassan jirgin, daya a Mossel Bay na kasar Afirka ta kudu daya kuma a tsibirin Rodrigues na tsibirin Moritiyas.

Mahakuntan kasar Ostareliya sun sanar a wannan Alhamis da gano wasu sassan jirgi da suka ce suna kyautata zaton na jirgin nan ne kirar MH370 da kamfanin Malesiya Airlines da ya yi batan dabo ranar takwas ga watan Maris na shekara ta 2014 da fasinjoji 239 a kan hanyarsa ta zuwa Pekin daga birnin Kuala Lumpur.

Cibiyar kula da harakokin tsaro a fannin sufuri ta kasar Ostareliya ta ATSB ta bayyana hakana ne bayan wani bincike da ta gudanar a kan sassan jirgi da aka gano, daya a Mossel Bay na kasar Afirka ta Kudu daya kuma a tsibirin Rodrigues na tsibirin Moritiyas da ke a yankin Tekun Indiya.

Dama dai a watan Maris da ya gabata mahukuntan kasar ta Ostareliya sun bayyana wasu sassa biyu na jirgi da aka tsinto a kasar Mozambik da kasancewa na jirgin na Malesiya Airlines.

Mahukuntan kasar Malaysiya da masu aikin bincike na Faransa sun bayyana cewa kafin gano wadannan sabbin sassan jirgi, kiran fiffiken jirgi da aka tsinto a watan Yuli a tsibirin Reunion shi ne hujjar daya tilo dake nuni da cewa jirgin na Malesiya Airlines ya nutse ne a ruwa.