An gano tarkacen jirgin saman fasinja da ya yi hadari a Nijeriya | Labarai | DW | 23.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano tarkacen jirgin saman fasinja da ya yi hadari a Nijeriya

Rahotannin baya-bayan nan daga Nijeriya sun ce bisa ga dukkan alamu mutane 117 dake cikin wani jirgin saman fasinja samfurin Boeing 737 da yayi hadari a Nijeriya sun mutu. Kungiyar ba da agaji ta Red Cross da kuma hotunan da gidan telebijin kasar suka bayyana ya nuna tarkacen jirgin da ya fado a kauyen Lisa na jihar Ogun mai nisan kilomita 30 arewa da birnin Legas. Hotunan dai basu nuna wata alama cewa akwai wanda ya tsira daga wannan hadari ba. A halin da ake ciki gwamnatin jihar Oyo ta nemi gafara game da rahotannin da ta bayar da farko cewa wasu daga cikin fasinjojin sun tsira. Jirgin na kamfanin Bellview ya na dauke da fasinjoji sama da dari daya ciki har da manyan jami´an gwamnatin tarayyar Nijeriya da kuma na kungiyar habaka tattalin arzikin Afirka Ta Yamma wato ECOWAS. To sai dai kawo yanzu ba´a bayyana sunayen su ba, kana kuma ba´a bayyana abin da ya haddasa hadarin ba. A jiya da daddare jirgin ya bace daga allon hasumiyar sarrafa zirga-zirgar jiragen sama ´yan mintoci kadan bayan tashinsa daga Legas zuwa Abuja.