An gano tarkacen jirgin saman da ya tarwatse a Cameroun
May 7, 2007Talla
Bayan rahottanin da su ka yi ta saɓawa da juna, a game da gano tarkacen jirgin saman da ya tarwatse a kasar Cameroun tsakanin daren juma´a, zuwa asabar da ta wuce, a halin yanzu dai ,bayyanai sun haƙiƙance cewar, babu shakka, masu aikin ceto, sun gano gawar wannan jirgi mallakar kampanin Kenya Airways, a kussa da birnin Douala.
A wani taron manema labarai, da shugaban kampanin Kenya Airways ya kira , ya bayana cewar, surƙuƙin itatuwa a yankin da hadarin ya faru, ya kawo matukar cikas wajen ayyukan gano jirgin.
Saidai ya zuwa yanzu, babu cikkaken bayyani, a game da yawan mutanen da su ka rasa rayuka ko su ka ji ranuka, daga jimilar mutane 114, da ke cikin wannan jirgin.