1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawawwakin mutane 198 a Indonesia

June 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6T

Rahotanni daga garin Sulawesi dake kudancin Indonesia na nuni dacewa,kawo yanzu mutane 198 suka rasa rayukansu a sanadiyyar ambayan ruwa da zaizazar kasa,ayayinda jamian agaji ke cigaba da ceto rayukan wadanda ke makale cikin tabo ,da sauran gawawwakin da baa gano ba.Mafi yawan mace machen sun auku ne ranar talata ,a yankunan gudana biyar sake wannan gunduwa,amma daga wannan lokaci kawo yanzu jamian ceto na gano gawawwaki,musamman a wasu yankuna da ke da wahalar isa.Rahotanan daya fito daga cibiyar agajin gaggawa na Indonesian na nuni dacewa ,mutane 198 aka gano gawawwakinsu,ayayinda har yanzu baa gano mutane 73 ba.

Kasar Indonesia dai na daya daga cikin kasashen duniya dake fama da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa ,wanda aka danganta da rashin kulawa da dashen itatuwa.A watan janairun daya gabata sama da mutane 150 suka suka rasa rayukansu a balain zaizayar kasa guda biyu a garin Java.