1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawarwakin wasu matasa shida a tashar jiragen kasa ta Duisburg

August 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuE3

Yan sanda a nan jamus sun gano gawarwakin wasu mutane 5 a wata tashar jirgi kasa a Duisburg an kuma harbe su a kawunansu.Mutum na shida kuma ya mutu kann hanyar zuwa asibiti sakamakon munanan raunuka da ya samu daga harbin bindiga.an dai samu gawarwakin mutanen ne cikin kanan motoci uku a gurin ajiye motoci dake babbar tashar jirgin kasan birnin na Duisburg.Ba dai san wadanda suka aikata wannan taasa ko dalilin yin hakan ba.