An gano gawar kwamandan Majalisar Dinkin Duniya a Haiti | Labarai | DW | 08.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano gawar kwamandan Majalisar Dinkin Duniya a Haiti

An gano gawar kwamandan rundunar kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Haiti a cikin otel dinsa. An gano gawar janar Urano Teixeira Bacellar dan kasar Brazil da harsashi a jikin ta. Jami´an MDD sun ce bisa ga dukkan alamu janar din ya kashe kansa da kansa. To amma rundunar sojin Brazil ta bayyana wannan lamari da cewa wani hadari ne na bindiga. Har yanzu dai kasar Haiti na fama da tashe tashen hankula shekaru biyu bayan kifar da gwamnatin shugaba Jean-Bertrand Aristide. A ranar juma´a da ta gabata, MDD ta yi kira ga gwamnatin wucin gadin kasar da ta kira zabe a ranar 7 ga watan fabrairu. Da farko an shirya gudanar da zaben ne a cikin watan nuwamban bara, amma aka dage shi har sau biyar.