An gano albarkatun mai da gas a Zambia | Labarai | DW | 23.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano albarkatun mai da gas a Zambia

A kasar Zambia,an gano albarkatun mai dana iskar gas a gunduwowin Chavuma da Zambezi daya yankin arewa maso yammacin kasar,kusa da kann iyakarta da Angola.Shugaba Levy Mwanawasa ya sanar da gano albarkatun mai akarkashin kasa bayan gwajin da akayi,a taron daya gudanar da manema labaru a Lusaka.Yace yanzu kamfanonin hakan mai zasu gudanar da bincike dangane adadin da zaa iya samu,kana zaa fadada binciken zuwa wasu gundumomin kasar ta Zambia.Rahotanni daga kasar na nuni dacewa tuni shugaba Levy Mwanawasa ya sanar da nada komitin albarkatun man petur ,domin gudanar da binciken albarkatun mai da iskar gas din da kamfanoni masu zaman kansu.