An gana tsakanin shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas da Praminista Isma´il hanniyeh | Labarai | DW | 15.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas da Praminista Isma´il hanniyeh

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, da Praminista Isma´il Hanniyeh, sun tantanna yau a zirin Gaza.

Wannan ganawa itace ta farko, tun watan Juni da ya wuce.

Magabatan 2, sun cenza miyau, a kan matakan maido da kwanciyar hankali mai dorewa, a Palestinu, mussamman a gabar da ake tsakanin magoya bayan Fatah da na Hamas.

Kazalika, sun tantana a game da girka gwamnatin hadin kan kasa, da zata kunshi bangarorin 2.

Abbas da Hanniyeh, sun yi bitar halin da Palestinu ke ciki,tun bayan kame sojan Isra ila, daya, ranar 25 ga watan juni, wanda a sakamakon hakan, rundunar Tsahal ta Isra´ila, ke ci gaba da barin wuta a kan al´ummomin yankunan palestinawa, wanda ya zuwa yanzu, su ka hallaka a kalla mutane 180.

A daya hannun, shugaban kasa da Praministan Palestinu, sun duba batun albashin ma´aikata, da gwamnati ta kasa biya tun hawan Hams bisa karagar mulki.

Masu sharhi a kan harakokin gabas ta tsakiya, sun danganta wannan haduwa, da wani mataki na dimke baraka, tsakanin Fatah da Hamas da su ka yaki juna a kwanakin baya.