An gana tsakanin shugaba Putin da Ali Larijani | Labarai | DW | 11.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin shugaba Putin da Ali Larijani

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da babban mai shiga tsakani a shawarwarin shirin nukiliyar Iran Ali Larija akan aikace aikacen nukiliyar kasar. Kamfanin dillancin labarun Interfax ya rawaito majiyoyin fadar Kremlin na cewa an yi ganawar ne a fadar shugaba Putin. Baya ga shirin nukiliyar Iran, mutanen biyu sun kuma shawarta akan huldodin tsakanin kasashensu da kuma batutuwa da suka shafi duniya baki daya. Bayan tattaunawar an jiyo ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov na cewa da akwai yiwuwar komawa ga tattaunawar na ta kasashe 6 akan shirin nukiliyar Iran nan ba da dadewa ba.