An gana tsakanin Olmert da Chirac a birnin Paris | Labarai | DW | 14.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin Olmert da Chirac a birnin Paris

FM Isra´ila Ehud Olmert ya sha alwashin yin duk iya kokarin ganin an koma kan teburin shawarwari da hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinawa. Olmert wanda yanzu haka yake ganawa da shugaba Jacques Chirac na Faransa a birnin Paris, ya ce dole ne a fara daina kaiwa Isra´ila hare hare kuma dole ne a girmama dukkan yarjejeniyar da aka cimma da Isra´ila tare da amincewa da ´yancin wanzuwar ta. Shi ma shugaba Chirac ya yi kira da a koma kan teburin shawarwari to amma yaki bai yi tsokaci ba game da shirin FM Olmert na shata kan iyakokin Isra´ila ita kadai. Olmert na rangadin kasashen Turai don neman goyon bayan ga wannan shiri na sa da ake takaddama akai tare da janyewa daga ilahirin yankin Yammacin Kogin Jordan ba tare da an cimma yarjejeniyar yin haka da Falasdinawa ba.