1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gana tsakanin Merkel da Olmert a birnin Berlin

December 12, 2006
https://p.dw.com/p/BuYA
Kwana daya bayan wani abin da kafofin yada labarun Isra´ila suka kira tuntube baki akan makaman nukiliya, FM Ehud Olmert ya ci-gaba da ziyararsa a birnin Berlin. Yanzu haka dai an gana tsakanin SGJ Angela Merkel da FM na Isra´ila, inda suka tattauna akan mawuyacin hali da ake ciki a yankin GTT. In jima kadan ne kuma Olmert zai gana da shugaban kasa Horst Köhler, inda zasu tattauna kan Iran da kuma fatan da ake na farfado da zaman lafiya da Falasdinawa. Tuni kuwa FM na Isra´ila ya dora furanni a tashar jirgin kasa ta Grünewald, inda daga nan ne aka yi jigilar dubban Yahudawa zuwa sansanonin gwale gwale. Yayin wata hira da wata tashar telebijin Jamus ta yi da shi jiya Olmert ya janyo kace-nace a gida sakamakon subutar bakin da yayi cewa Isra´ila na mallakar makaman nukiliya. Kawo yanzu Isra´ila ta ki fitowa fili ta tabbatar ko ta musanta cewa tana da makaman nukiliya.