An gana tsakanin magoya bayan Joseph kabila da na Jean Pierre Bemba | Labarai | DW | 29.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin magoya bayan Joseph kabila da na Jean Pierre Bemba

A birnin Kinshasa na Jamhuriya Demokradiyar Kongo, an gana yau tsakanin tawagogin shugaban ƙasa, Joseph kabila, da mataimakin sa, Jean Pierre Bemba.

An yi wannan haɗuwa, bisa jagorancin wakilin musaman na Majalisar Dinkin Dunia, Wiliam Swing.

Burin wannan taro, shine samar da masalaha tsakanin ɓangarorin 2.

Dakarun shugaban ƙasar, da na mataimakin sa, sun gwabza da juna, a birnin Kinshasa,jim kaɗan, bayan hiddo sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, zagaye na farko.

Wannan itace haɗuwa ta farko, tsakanin ɓangarorin 2, tun bayan wannan tashe tashen hankulla da su ka hadasa mutuwar a ƙalla mutane 23.

A sakamakon taron an girka wani komitoci guda 2.

Komitin farko, zai bincike a kan mussababin ɓarkewar rikicin makon da ya gabata, sai kuma na 2, zai tunani a kan mattakan samar da zaman lahia, ta yadda zagayen zaɓe na gaba, tsakanin yan takarar 2, ya wakana salin-alin.

Magoya bayan Kabila da na Jean Pierre Bemba, sun yi alkawarin bada haɗin kai, domin cimma burinda aka sa gaba.