1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gana tsakanin Joseph Kabila da Jean Pierre Bemba.

Yahouza S.MadobiSeptember 14, 2006

Tun bayan zaɓen watan Yuli an yi ganawar farko tsakanin Joesph kabila da Jean Pierre Bemba

https://p.dw.com/p/BtyA
Hoto: picture alliance /dpa

An yi ganawar farko ƙeƙe da ƙeƙe, tsakanin shugaban ƙasar Kongo Joseph Kabila da mataimakin sa ,Jean Pierre Bemba,tun bayan zaɓɓuɓukan da su ka wakana a ƙarshen watan Juli da ya gabata.

An yi wannan ganawa albarkacin ziyara aiki da komishinan harakokin wajen Ƙungiyar gamayya turai, Havier Solana ya kai a Jamhuriya demokradiyar Kongo, da zumar ɗumke ɓaraka da ta biyo bayan sakamakon zaɓɓuɓukan da su ka gudana, ranar 30 ga watan Juli da ya wuce.

Idan dai ba a manta ba, jim kaɗan bayan bayana wannan sakamako, rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Joseph kabila, da na Jean Pierre Bemba, yan takara da su ka yi nasara shiga zagaye na 2, na zaɓen shugaban kasa.

A tsawan sa´o´i 2 shugabanin sun tantana a game da matakan warware rikicin da ya haɗa su cikin ruwan sanhi da kuma hanyoyin shirya zaɓe na gaba cikin kwanciyar hankali da fahintar juna.

Rahotani daga Kinshasa sun ce Joseph Kabila da Jean Pierre Bemba sun cimma daidaito ta wannan fanni, to saidai masharahanta sun nunar da cewa, wannan alkawura ne kawai,, na fatar baka, ta la´akari da yadda dakarun shugabanin 2, ke ciki shirin ta kwana.

Ƙungiyar gamayya turai da ta bada kasso mafi tsoka a shirye shiryen zaɓen ta bukaci ɓangarori 2, su cimma matakan tabbatar da zaman lahia mai ɗorewa.

Jim kaɗan bayan taron shugabanin, hukominin zartaswa na jam´iyun su sun kiri tarruruka, da zumar tantanawa a game da yiwuwar tabatar da yarjejeniyar da magabatan su ka cimma.

Saidai duk da nasara da aka samu ta shirya zaɓen har yanzu ba ta cenza zane ba, ta fannin tsaro, inda yan bingida daɗi ke ci gaba da kai farmaki da fyaɗe ga mata, a yankunan daban-daban, kamar yadda sakataran hukumar bada agaji ta MDD ,Jan Egeland ya bayyana a wata ziyara aiki da ya kai ƙasar.

A gani na, wannan itace ƙasar da ta yi fice a faɗin dunia ta fannin yiwa yaya mata fyaɗe.

Ban taɓa ganin wanni yanki ba a ɗoran ƙasa baki daya,inda mata ke ganin ukuba kamar Jamhuriya Demokradiyar Kongo.

Ba´ada bayan shinfida demokradiya inganttata magance matsalolin fyaɗe da na sojojin sa kai barkatai cikin ƙasa na daga ƙalubalen da sabuwar gwamnati z ata fuskanta.

A nasa ɓangare duk da rikicin da ke wakana,Havier Solana, ya yi imanin cewar, Jamhuriya Demokradiyar Kongo, na bisa turba ta gari, a fannin girka demokradiya.