An gana tsakanin Janar Swei na Myanmar da wakilin MƊD Ibrahim Gambari | Labarai | DW | 02.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin Janar Swei na Myanmar da wakilin MƊD Ibrahim Gambari

Shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Burma ko kuma Myanmar Janar Than Swei a yau talata ya gana da wakilin MDD na musamman Ibrahim Gambari. Kamar yadda wani jami´i a ma´aikatar yada labaru ya nunar, Gambari ya gabatarwa janar din fushin kasashen duniya a dangane da murkushe zanga-zangar neman demukiradiya. Amma da farko wani kakakin MDD ya ce Gambari zai nemi shugabannin gwamnatin mulkin sojin da su daina daukar matakan murkushe zanga-zangar lumana da ake yi sannan su saki mutanen da aka kama kana kuma su aiwatar da canje canje na demukiradiyya.Jami´an diplomasiya na ketare sun ce mutanen biyu sun gana ne a yankin karkara na Naypyidaw dake zaman hedkwatar gwamnatin mulkin sojin.