An gana tsakanin Janar Swei na Myanmar da wakilin MƊD Ibrahim Gambari
October 2, 2007Talla
Shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Burma ko kuma Myanmar Janar Than Swei a yau talata ya gana da wakilin MDD na musamman Ibrahim Gambari. Kamar yadda wani jami´i a ma´aikatar yada labaru ya nunar, Gambari ya gabatarwa janar din fushin kasashen duniya a dangane da murkushe zanga-zangar neman demukiradiya. Amma da farko wani kakakin MDD ya ce Gambari zai nemi shugabannin gwamnatin mulkin sojin da su daina daukar matakan murkushe zanga-zangar lumana da ake yi sannan su saki mutanen da aka kama kana kuma su aiwatar da canje canje na demukiradiyya.Jami´an diplomasiya na ketare sun ce mutanen biyu sun gana ne a yankin karkara na Naypyidaw dake zaman hedkwatar gwamnatin mulkin sojin.